Siyasa

Munafiki Allah Ne Ya Tashi Kamaka: Davido Yayi Martani ga Hakimin Buhari Da Yasha Kayi a Zaben Kano

Fitaccen mawakin Najeriya, Davido, ya zolayi tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC.

Mista Ahmad, wanda ya nemi takarar tikitin dan majalisa mai wakiltan mazabar Gaya/Ajingi/Albasu/ a majalisar tarayya, ya samu kuri’u 16 kacal inda ya sha kaye a hannun Abdullahi Gaya wanda ya samu kuri’u 109 a zaben fidda gwanin.

Munafiki Allah Ne Ya Tashi Kamaka: Davido Yayi Martani ga Hakimin Buhari Da Yasha Kayi a Zaben Kano

Da yake martani ga kayen da Ahmad ya sha, mawakin ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Allah ne ya kama tsohon hadimin shugaban kasar.

Ya kwatanta lamarin da abun da ya faru a zaben jihar Osun, yana mai cewa duk abun da mutum ya shuka ita yake girba.

“Ya batun zaben Osun…..Duk abun da mutum ya shuka shi yake girba”

Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano
Tuni dai Ahmad ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin sannan ya nemi a sake gudanar da sabon zabe.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, Bashir ba zai amince da sakamakon zaben ba domin abubuwan da suka faru a wurin zaben sun janyo cikas na inganci da nagartan zaben, kuma idan ya yi shiru bai yi wa mutanensa da jam’iyyar APC adalci ba.

A cewarsa, an hana mafi yawa cikin daliget dinsa shiga wurin zaben ballantana su kada kuri’arsu, sannan babu wata takardan zabe dauke da sa hannun wakilansa don ba a bari ma sun shiga wurin zaben ba.

Aika Da Wannan Labarin: