Kasuwanci

Muna neman mafita ga karancin man fetur, kuyi hakuri da mu – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci yan Najeriya da su yi hakuri yayin da gwamnatin ke neman “mafita ta dindindin” kan karancin man fetur (PMS) a kasar.

Timipre Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur, yayi wannan roko a ranar Lahadi a wata sanarwa da Horatius Egua, babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa ya fitar.

Ministan ya ce gwamnati na sane da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon karancin.

Advertisement

“A makonnin da suka gabata ‘yan Najeriya sun yi ta fama da karancin man fetur, ba don rashin wadatar kayayyaki ba amma saboda gazawar tantancewa, wanda ya ba da damar gurbatattun kayayyaki shiga cikin kasar,” inji shi.

Advertisement