Tsaro

Mun yi asarar sojoji 498 a Ukraine – Rasha

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana adadin sojojin ta da aka kashe a kasar Ukraine tun bayan fara yakin.

Ma’aikatar ta bayyana cewa “Sojojin Rasha 498 ne suka mutu tun ranar alhamis” lokacin da yakin da shugaban kasar Vladimir Putin ya ayyana.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta ce “karin wasu sojojin Rasha 1597 sun jikkata.”

Advertisement

Ma’aikatar ba ta bayyana yanayin raunin da aka samu ba.

Putin ya ba da umarnin kai farmakin soji kan makwabciyarsa saboda yunkurin NATO.

An cigaba da gwabza fadan da aka fara a makon jiya alhamis, duk kuwa da yunkurin gudanar da tattaunawar sulhu.

Yayin da ake ci gaba da gwabzawa, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, IAEA, Rafael Grossi, ya nakalto bayanai daga birnin Moscow, ya ce sojojin Rasha na da iko da babbar tashar makamashin nukiliya ta Ukraine.

A halin da ake ciki kuma, Rasha ta ja kunnen kungiyar tsaro ta NATO game da shiga cikin yakin da ake yi da Ukraine.

Advertisement