Labarai
Mun Jima Da Sakin Murja Kunya – Kakakin Gidan Yari
“Tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata mu ka saki Murja Kunya daga cikin gidan yari bayan ta cika ƙa’idodin belin” – Inji kakakin gidan yari.
Kakakin gidan gyaran hali (Gidan Yari) na jihar Kano AC Misbahu Kofar Nasarawa ya shaidawa manema labarai ciki har daJaridar Daily Nigeria cewa sananniyar ‘yar Tiktok Murja Kunya ba guduwa ta yi daga gidan yari ba.
A cewar kakakin, tun ranar Alhamis din da gabata Murja ta cika ƙa’idodin belin ta, kuma a ka sake ta a wannan ranar.
Ya ƙara da cewa kotu ce ta kawo ta ajiya a gidan yarin, kuma kotu ce ta ce su sake ta, saboda haka babu dalilin ci gaba da tsare.