Labarai

Mujiya Ta Maƙale A Wurin Ɗaura Lambar Mota

Wata mujiya ta kwana kanta makale a bayan wata lambar mota bayan da motar ta buge ta.

Masu motar suna tuƙi a kusa da Laxfield, Suffolk ranar 5 ga Satumba, lokacin da suka ga mujiya tana shawagi a kusa amma ba su ankara ba sun bugi tsuntsun ba.

Sai dai washe gari suka tarar da mujiyar a rataye a gaban motar.

An kaiujiyar Suffolk Owl Sanctuary inda take samun sauki.

A lokacin da aka yada hotunan mujiyat a Facebook a ranar Alhamis, Stonham Aspal, sun ce masu motar “sun fito ne don gano wannan mujiya mara sa’a da kanta makele a bayan plate number din, tayi sa’a sosai da ta rayu”.

“Alhamdu lillahi, da alama bai yi kokawa da yawa ba kuma baya ga ciwon kai, ba shi da wasu raunuka,” in ji mai magana da yawun.

Ana kula da mujiya a asibitin raptor inda suka ce suna fatan zata samu cikakkiyar lafiya.

Free Bonus

X