Siyasa

Motocin dauke da makamai sun shiga Tripoli don goyon bayan Fara-ministan rikon kwarya, Dbeibah

A jiya asabar ne ayarin mayakan suka shiga birnin Tripoli daga birnin Misrata na kasar Libya, domin baiwa firaministan rikon kwarya goyon baya, a dai dai lokacin da majalisar dokokin kasar ke yunkurin tsige shi daga kan mukamin shi domin goyon dan takarar majalisar.

Firaministan rikon kwarya Abdulhamid Dbeibah ya lashi takobin mika mulki ne kawai bayan zabe ya kuma yi watsi da matakin da majalisar dokokin kasar ta dauka a wannan makon na nada tsohon ministan cikin gida Fathi Bashagha ya jagoranci sabuwar gwamnati.

Zuwan ayarin motocin ya nuna hatsarin sake barkewar fada a kasar Libya a daidai lokacin da rikicin ke ci gaba da ruruwa, biyo bayan wani gangami a makonnin baya-bayan nan da bangarorin da ke dauke da makamai ke goyon bayan bangarorin siyasa daban-daban.

Advertisement

Ayarin motocin na ranar Asabar da suka hada da motoci sama da 100 a cewar wani shaida na Reuters, sun isa ne bayan Dbeibah a ranar Asabar din da ta gabata ya zargi majalisar dokokin kasar da “daukar alhakin duk wannan zubar da jini da hargitsi” da aka yi a Libiya cikin yan shekarun nan.

Kakakin majalisar, Aguila Saleh, ya zargi Dbeibah da cin hanci da rashawa da kuma neman yin amfani da mukaminsa don biyan bukatun kansa, maimakon aiwatar da sauyi mai ma’ana.

Kasar Libya dai ba ta da kwanciyar hankali tun bayan boren da kungiyar tsaro ta NATO ta yi wa Muammar Gaddafi a shekara ta 2011 kuma ta rabu a shekara ta 2014 tsakanin bangarorin gabashi da yamma.

Advertisement