Al'ummaLafiya

Ministar Buhari, Sadiya Farouq Ta Tafi Ƙasar America Wajen Haihuwa

Sadiya Farouq

Ministar Agajin Gaggawa, Masifu da Cigaban Jama’a Sadiya Umar Farouq ta je kasar Amurka domin haihuwa. Jaridar Street Journal ta ruwaito.

Farouq wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2019, ita ce mafi karancin shekaru a majalisar ministocin shugaban kasa.

Tarihinta da shugaban kasa ya samo asali ne tun daga tsohuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change CPC a lokacin Farouq tana rike da ma’ajin jam’iyyar na kasa.

Advertisement