Labarai

Meta Ya Rufe Shafin Instagram Da Facebook Na Khamenei Bisa Jinjinawa Hamas

Meta ya cire shafukan Instagram da Facebook na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei bayan sukar da ake masa na goyon bayan Hamas.

Meta bai bayar da takamaiman dalilin daukar matakin ba amma ya ce an cire shafukan ne saboda “suna keta manufofin gudanarwar kamfani, kuma suna da hadari ga daidaikun mutane”.

Dangane da manufofin da aka bayyana, Meta na tushen fasaha na California ta ƙasar Amurka ba ya ƙyale shafuka waɗanda “suna shelar tashin hankali ko kuma suna yin tashin hankali kuma su kasance a kan dandamalin mu.”

Khamenei da shafukan da ke da alaka da shugaban na Iran sun bayyana goyon bayansu ga harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya kashe mutane kusan 1,200.