Addini

Mawaƙin Da Yayi Ɓatanci Ga Annabi [S.A.W] Aka Yanke Mai Hukuncin Kisa, Ya Ɗaukaka Ƙara

Wani mawaki Yahaya Sharif-Aminu da aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2020 bisa samun shi da laifin yin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W), ya roki kotun kolin Najeriya da ta soke hukuncin da aka yanke mai. Hakan ya fito ne a cikin bayanan kotu da SaharaReporters ta samu a ranar Laraba daga lauyan shi, K. Alapinni.

A bisa bayanan, Sharif-Aminu yana neman kotun koli ta yanke hukuncin cewa abin da ya aikata ba laifi ba ne a dokokin Najeriya.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, ta bayyana cewa an baiwa Abdullahi Ganduje da Musa A. Lawan takardun kotu game da karar. Haka zalika, kotun Shari’a ta yanke wa mawakin hukuncin kisa, wanda kotun koli ta soke shi. Duk da haka, saboda sabani da aka samu a shari’ar da ta gabata, ta ba da damar sakin mawakin, ta kuma bukaci a saurare shi a gaban wani alkalin kotun Shari’a na daban.

Advertisement

Sharif-Aminu ya roki kotun daukaka kara da ta janye hukuncin da aka yanke na a sake shi kan aikata sabo. Lauyan shi yayi ikirarin cewa a sake shi daga tsare. Yana neman a ba shi odar bayar da wannan kara, tare da yin watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, sannan ya yanke hukunci a kan wanda ya kai karar.

Advertisement