Labarai

Matukin Keken Napep Ya Rasa Ran Shi Kan Kudin Haraji Naira N400

Rikicin da ya barke tsakanin wani ma’aikacin kwamitin tattara kudaden haraji da wani matukin babur mai uku kan rashin biyan harajin Naira N400 a kowace rana yayi sanadiyar mutuwar mutakin Keken Napep din a ranar Larabar da ta gabata a garin Sapele da ke karamar hukumar Sapele ta jihar Delta.

A yayin da ake fafatawa, yaron mai bada tikitin harajin, wanda aka bayyana sunansa da Tunde, amma wanda ake kira da Osama, ya rike mai Keken Napep din mai suna Augustine Williams a wuyansa.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya fadi kuma ya mutu a wani asibiti da ke kusa, inda aka kai shi domin kula da lafiyarsa.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa DAILY POST cewa rikicin ya faro ne a lokacin da Osama yayi yunkurin kwace mukullin matukin babur, wanda ya haifar da zazzafar muhawara.

“An yi gwabzawar ne a lokacin da Osama yayi yunkurin cire makullin Keken Napep din, kuma Augustine ya rike hannunsa. Lamarin ya rikide zuwa fada, inda Osama ya cafko wuyan Augustine, wanda hakan yasa ya fadi.” Inji wani ganau.

Da yake nuna takaicin wannan abin takaicin, wani hamshakin attajirin kasuwanci, Ese Agbamitor, ya bayyana cewa a koda yaushe ma’aikatan na fuskantar cin zarafi da wasu nau’o’in hare-hare daga jami’an hukumar tattara kudaden haraji.

Advertisement