Siyasa

Matawalle ya nada sabon mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Bello Matawalle wanda shine gwamnan zartaswar jihar Zamfara ya nada sabon mataimakin gwamnan jihar mai suna Hassan Gusau, wanda hakan ya biyo bayan tsige Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Hassan Gusau wanda shine mataimakin gwamnan jihar Zamfara mai ci ya kasance tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Sanata ta tsakiya a majalisar dokokin kasar. Nadin nasa ya biyo bayan tsige Aliyu Gusau da majalisar dokokin jihar ta yi a yayin zaman majalisar.

Mustafa Kaura wanda shi ne kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya ce an samu tsohon mataimakin gwamnan da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa. Kakakin majalisar dokokin jihar Nasiru Mu’azu Magarya ne ya dauki nauyin gaya wa ‘yan majalisar da su ci gaba da kada kuri’ar rashin amincewa da shi wanda har ya kai ga tsige shi.

Advertisement
Advertisement