Laifuku

Matashi Zai Shafe Shekaru 20 A Gidan Yari Da Tarar Dubu 50, Bisa Laifin Yanke Wata Mata Da Wuka Da Kama Nonon Ta

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yankewa wani matashi dan shekara 20, Bashir Yahaya, daurin shekaru 20 a gidan yari bisa samun shi da laifin yunkurin kisan kai.

Mista Yahaya, wanda ke zaune a Kabuga Quarters, Kano, an tuhumi shi ne da laifin rashin da’a, wanda ya jawo mummunan rauni da kuma yunkurin aikata kisa, NAN ta bayyana.

Mai shari’a Suleiman Baba-Namallam ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin nasa ba tare da wata shakka ba.

Advertisement

Alkalin kotun ya yanke wa Mista Yahaya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari tare da biyan tarar Naira 20,000 bisa laifin rashin da’a.

Mista Baba-Namallam ya kuma yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin shekaru bakwai da tarar Naira 30,000 bisa samun shi da laifin yin mugun nufi.

Ya kuma yankewa Mista Yahaya hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda yunkurin kisan kai.

Alkalin ya ce hukuncin zai gudana ne a lokaci guda.

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Zahraddeen Kofar-Mata, ya sanar da kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Mayu, 2019, a Tal’udu Quarters, Kano.

Mista Zahraddeen ya ce wanda yake aiki ya aike da mai laifin domin ya baiwa ma’aikaciyar shi, Aisha Kabir ‘yar shekara 20 abincin buda baki a asibitin Orbit Dental Clinic Tal’udu Quarters Kano.

“Bayan ya ba ta abincin, A’isha ta roki mai laifin da ya kunna injin janareta saboda babu wutar lantarki.

“Maimakon tayar da injimin, wanda aka yanke wa hukuncin ya damko nonon A’isha ya kuma yi mata barazana, ya yi garkuwa da ita ta hanyar amfani da wuka mai kaifi.

“Ya yi mata mummunan ya ka sannan ya karbi wayar ta,” in ji shi.

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa daga baya wani Zayyanu Abdulhamid ne ya same ta a kwance cikin jini.

Ya ce an garzaya da A’isha zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin yi mata magani.

Mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu hudu don tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake tuhuma.

Wanda aka yanke wa hukuncin ya kare kan shi kuma ya musanta aikata laifin.

Lauyan da ake kara, II Abubakar, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar wannan shi ne laifin da ya fara aikatawa, kuma ya roki kotun da ta yi adalci da rahama.

Advertisement