Al'umma

Matashi yayi yunkurin tura kan shi lahira ta hanyar shan guba, akan masoyiyar shi ta guje shi

Saurayi yayi yunkurin aika kan shi barzahu ta hanyar shan guba, saboda kawai masoyiyar shi ta guje shi Baya a Jihar Kano

Da yammacin yau Talata ne, wani matashi Tijjani Abubakar ɗan asalin unguwar Gama PRP dake yankin karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano ya yi yunkurin hallaka kan sa biyo bayan cin amanar sa da masoyiyarsa ta yi.

Majiyar mu, Aminci Radio Kano ta rawaito matashin ɗan kasuwa sayar da wayar hannu ta Farm Centre ya yi wannan yunƙurin ne bayan budurwar da ya shirya angoncewa da ita ta ce a kai kasuwa, domin ta samu wanda ya fishi iya tattali da soyayya, baya ga maƙudan kudade da yake kashe mata.

Advertisement
Advertisement