Matashi Ya Rasa Ransa Wajen Satar Wayar Wutar Lantarki
Wani matashi da ba a bayyana sunansa ba ya haɗu da ajalinsa a garin Gashuwa jihar Yobe, a cikin mahadar wutar lantarki (Transformer).
Ana zargin cewa wannan mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin a unguwar Zangon Takari kusa da Video Centre a cikin garin Gashuwa, inda wutar lantarki ta yiwa matashin shokin a yayin da yake yunkurin yanke wayar mai tsada ta cikin mahadar wutar lantarki ɗin da ake kira da (Amor cable), inda nan take ya mutu.
Mazauna unguwar sun shaidawa manema labarai cewa, su dai kawai sun wayi gari da ganin gawar matashin a cikin mahadar wutar lantarkin, kuma da aka duba sai aka ga ya mutu ne a yayin da yake yanke wata wayar wuta, inda ya gamu da ajalinsa a wannan hali a yayin da aka maido wutar lantarki ba ba zato babu tsammani .