Siyasa

Matar tsohon gwamna Obiano, Ebelechukwu, ta mari Bianca Ojukwu a wajen bikin rantsar da Soludo

Wata dirama ta barke a ranar Alhamis a wurin bikin rantsar da Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan jihar Anambra lokacin da uwargidan gwamna Willie Obiano mai barin gado, Ebelechukwu ta mari Misis Bianca Ojukwu a wajen taron.

Wakilin NAN da ke wurin taron ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan da aka rantsar da Soludo.

Tuni dai manyan baki da suka hada da Obiano suka zauna a lokacin da Mrs Obiano ta shiga sannan ta zarce a layin gaba inda matar Dim Odumegwu Ojukwu ta zauna tare da marin ta.

Advertisement

Matakin ya ja hankalin jami’an tsaro da wasu mutane da suka janye Misis Obiano daga hannun Bianca wadda ta yi matukar kaduwa da marin.

Daga baya an tafi da Mrs Obiano, kuma jim kadan, mijin nata ya bar wurin tun da lamarin ya faru bayan an rantsar da sabon gwamnan.

Arewa Times Hausa ta ruwaito cewa babban alkalin jihar, Mai shari’a Onochie Anyachebelu ne ya rantsar da Soludo da misalin karfe 9:45 na safe a fadar gwamnatin jihar Anambra.

Advertisement