Lafiya

Matar da ta rayu da almakashi biyu a cikin ta har tsawon shekaru 20

Matar mai suna Bachena Khatun, mai shekara 55 a duniya, ta yi ta fama da lalluran ciwon ciki, biyo bayan tiyatar cire tsakuwa a wani asibiti da ke Chuadanga a shekarar 2002 da akayi mata.

Bayan kwanaki kaɗan ta fara jin zafi a cikinta, sai ta koma asibitin, sai wani likitan fiɗa da ya duba ta da wasu likitoci biyu da suke kula da su yayin aikin, ya yi watsi da matsalarta yana cewa, ciwon ba wani abin damuwa ba ne ta kwantar da hankalinta.

Biyo bayan kwaje-kwaje da akayi mata, likitoci sun bada shawarar a karshe a dauki hoton cikinta, inda aka gano almakashi biyu da aka manta a cikinta, bayan an yi mata tiyatar farko shekara 20 da suka wuce.

Advertisement

Likitan tiyata, Dokta Jawaherul Islam ya ce, an kafa wani kwamiti mai mutum uku da zai binciki yadda almakashin biyu suka kasance a cikin Bachena na tsawon lokaci.

Daga: Radiya Maburya.

Advertisement