Al'umma

Mataimakin sufeto janar na ƴan sanda yace sabuwar dokar sanya tufafin ƴan sanda mata ƙabilancin addini ne

Mataimakin Sufeto Janar na yan sanda Parry Osayande mai ritaya yayi zargin amincewa da sanya hijabi ga jami’an yan sanda mata da Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba yayi ba bisa ƙa’ida ne ba.

Advertisement

Sabuwar ka’idar ta kuma baiwa jami’an mata damar sanya yan kunne na ingarma a karkashin hujabin su ko kololuwar hula yayin da suke cikin kakin na ƴan sanda.

Osayende, a wani taron manema labarai a Benin, jihar Edo a ranar Larabar da ta gabata, ya bayyana sabbin ka’idojin sanya tufafin ‘yan sanda mata da aka amince da su a kasar a matsayin wanda ya sabawa ka’ida.

Advertisement

Yace, “Duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar na 1999 an dorawa yan Najeriya shi, amma hakan bai bai wa IG damar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da amfani da hijabi, wanda shi ne tsarin sanya suturar yan sandan Najeriya da Musulmi ke yi. Bai kamata yan sanda su kasance da launin kabilanci da addini ba.

“Kundin tsarin mulkin Najeriya shi ne doka mafi kololuwa a kasar, kuma kundin tsarin mulkin kasar ya ce idan wata doka ta saba wa kundin tsarin mulki, wannan doka za ta zama banza.

“Akwai wani bangare na Kundin Tsarin Mulki da ya kafa Majalisar Ƴan sandan Najeriya, wadda ke da Shugaban kasa a matsayin shugaba; tana da shugaban hukumar yan sanda a matsayin mamba sannan kuma gwamnonin jihohi 36 ma membobi ne. Wadannan ne kawai suke da yancin da tsarin mulki ya ba su damar amincewa da ka’idojin sanya tufafi ga yan sandan Najeriya.”

Yayi zargin cewa shirin gwamnatin shi ne a musuluntar da Najeriya kuma ya yi gargadin cewa irin wannan mataki na da hadari da kuma sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

“Amfani da hijabi sabawa kundin tsarin mulkin kasa ne, kuma idan kana gwamna ne kuma ka karya kundin tsarin mulkin kasa, tsigewa ne. Idan kai Shugaban kasa ne, tsigewa ne. Idan Babban Lauyan Gwamnati bai san aikinsa ba, dole ne wani ya koya masa,” inji shi.

Advertisement