Siyasa

Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Harabar Ofishin APC Na Akan Rikicin Shugabancin Jam’iyyar Na Bauchi

Wasu ƴa’ƴan jihar Bauchi dake arewacin Nigeriya sun gudanar da zanga-zanga zuwa sakatariyar jam’iyyar APC mai mulki a harabar ofishin ta na ƙasa, inda suka bukaci gwamna Mai Mala Buni da ya sa baki cikin gaggawa kan zargin tsige shugaban jam’iyyar na jihar a babban taron jam’iyyar na jihar da aka gudanar a kwanakin baya.

Masu zanga-zangar dai sun zargi Ministan Ilimi, Adamu Adamu da hannu a kan wannan turka-turkar siyasar, inda suka yi gargadin cewa matukar dai ba’a warware wannan naɗin da aka yiwa sabon ciyaman na jihar, APC za ta sake rasa jihar a zaɓen 2023.

Ƙarin bayani na nan tafe…….

Advertisement