Kasuwanci

Masu Saka Hannun Jari Na Cryptocurrency Sun Yi Asarar Miliyan $400 Ga Masu Kutse – Lazarus

Sabon rahoton Cryptocurrency na tsawon shekarar 2021 ya nuna cewa kasuwar kuɗaɗen dijital ba ta da ƙarfi don saboda barazana daga Koriya ta Arewa bayan jerin hare-hare ta hanyar kuste da kumasauran hanyoyi.

Phishing shine aikin sake kwafin gidan yanar gizo, kamar dandamalin shiga musayar crypto, don yaudarar masu amfani da ba su ji ba don ba da cikakkun bayanan su zuwa shafin shiga mara kyau.

An yi amfani da wannan hanyar, gami da malware (virus) da injiniyan zamantakewa a cikin hare-hare daban-daban guda bakwai kan kamfanonin saka hannun jari da musayar kudade a bara, galibi ta hanyar masu satar bayanai, inji Lazarus, da aka ruwaito sun haɗa da Koriya ta Arewa.

Advertisement

A cewar rahoton na crypto tracker, Chainalysis, hare-haren bakwai an kiyasta darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 400 na cryptocurrency, tare da tura kudaden zuwa asusun da ke da alaƙa da Koriya ta Arewa.

An takaita samun damar shiga kasuwannin hada-hadar kudi na kasar ta hanyar takunkumin Amurka da kawayenta, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa Koriya ta Arewa ta haifar da kutse a kasuwar crypto.

An tattaro cewa ana karkatar da kudaden da aka sace daga hare-haren zuwa cikin shirin makamashin nukiliyar Koriya ta Arewa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, sannan kuma ana amfani da su wajen ciyar da tattalin arzikin kasar Asiya.

“Aikin yaki da cibiyoyin hada-hadar kudi da gidajen musayar kudi” na gudana ne karkashin gwamnatin shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, in ji MDD a bara.

Su ma bankunan ba su tsira ba, inda ma’aikatar shari’a ta Amurka ta tuhumi wasu ‘yan Koriya ta Arewa uku da hannu a satar dala biliyan 1.3 na masu ba da lamuni da kamfanoni a duniya.

An kuma zargi Koriya ta Arewa da hada baki a cikin dijital heists na cryptocurrency.

Advertisement