Taskar Labarai

Masoyan Ummi Rahab sunshiga Damuwa ganin cewar Mijinta yanada wata matar kafin ita

Masoyan Ummi Rahab sunshiga Damuwa ganin cewar Mijinta yanada wata matar kafin ita

Masoyan jaruma Ummi Rahab dai sunshiga damuwa tun bayan wani rahoto daya fito na cewar mijinta Lilin Baba yanasa wata matar kafin ya auri Ummi Rahab.

Saidai masoyan jaruma Ummi Rahab sunyita nuna rashin jindadinsu a kafofin sada zumunta inda suke fadin cewar baikamata ace yadda takeda kyau haka ace mai mata zata aura ba.

Alhamdulillah a cikin satin nan ne aka daura auren Jarumar Kannywood Ummi Rahab da kuma masoyinta mawaki Lilin Baba, wanda ranar da akayi shine 18 ga watan June 2022.

An daura auren masu ne a wani masallaci dake Nepa office, da misalin karfe 11 na rana, a unguwar tudun murtala dake Kano, abisa sadaki naira 200,000.

Jarumi Ali Nuhu shine wanda ya karbarwa Lilin Baba Auren, ma’ana shine yayi masa walicci. Kuma da chan shine Wanda yakai sadakin achan kwanakin baya.

Mujallar kannywood ta fimmagazine ta bayyana cewa:

“Ya na da uwargida, wata ‘yar garin Jos wadda su ke da ɗa ɗaya da ita. Wata majiya ta ce yaron har ya girma, ya na zuwa makaranta.

“Ummi Rahab a kaduna zata zauna, kuma Lilin Baba ya gina wa Ummi gida a jikin gidan da uwargidan sa ta ke, kowacce da get ɗin ta. Kuma duk gidajen nasa ne na kan sa, ba haya ba ne.”

Back to top button