Siyasa

Martanin manyan shugabannin duniya (8) akan mamaye Ukraine da Rasha ta yi

Manyan kasashe irin su Amurka da Birtaniya da kuma Tarayyar Turai sun yi kakkausar suka kan tsoma bakin Rasha a Ukraine. Sun kuma jagoranci yunkurin kakabawa Rasha takunkumi da aika makamai zuwa Ukraine.

Advertisement

Sai dai martanin da Rasha ta mayar ya sha banban.

A cikin wannan labarin, za mu yi dubi ne kan matsayin manyan kasashen duniya da kuma abin da shugabannin su ke cewa game da tsoma bakin Rasha a Ukraine.

Advertisement

1. China: Shugaba Xi Jinping bai ce komai ba game da mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine na, amma ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar da sanarwa.

Babban abin da kasar Sin ta mayar da hankali kan yakin shi ne shiru da shugaba Xi Jinping ya yi – maimakon haka, sakataren harkokin wajen kasar ya fitar da sanarwa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 25 ga watan Fabrairun nan, Beijing ta ce ta amince da “mutunta yancin kan kasa da ikon mallakar yankuna na dukkan kasashe”, kuma ta bayyana cewa Rasha na da “mummunan matsalolin tsaro” da ya kamata a dauka da muhimmanci. “

Amma ya zuwa yanzu kasar Sin ba ta yi amfani da kalmar “kutse” ba – kan batun matakin da Rasha ta dauka a Ukraine.

Masu sharhi kan harkokin diflomasiyya ba su yi mamakin shawarar ba, inda suka ce a ranar 4 ga watan Fabrairu, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaran shi na Rasha Vladimir Putin sun gana a birnin Beijing – ganawar su ta 38 tun daga shekarar 2013.

Shugabannin biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa suna kira ga kasashen yamma da su yi watsi da akidar su ta yakin cacar baka. Xi yayi suka musamman game da fadada NATO zuwa Turai.

Abin da ya fi fitowa fili shi ne, China ta ki kada kuri’a a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don yin watsi da tsoma bakin Rasha a Ukraine.

2. Indiya: Sa’o’i kadan bayan da Rasha ta mamaye kasar Ukraine, wani sako ya fito daga Indiya ta hannun ministan harkokin cikin gidanta Rajkumar Ranjan Singh, yana mai cewa kasar ba ta damu da lamarin ba.

Sai dai kasar ta kaurace wa kada kuri’a a taron kwamitin sulhu na MDD kan batun. Rasha da Indiya sun dade suna da alaka ta tsaro, amma firaministan Indiya Narendra Modi na tuntubar shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky.

A ranar 26 ga Fabrairu, Firayim Minista Modi yayi kira da “kowace gudunmawar da za ta iya bayarwa ga shirin zaman lafiya”, a cewar kakakin gwamnati.

3. Turkiyya: Gwamnatin Shugaba Erdogan ta soki mamayar amma ta ce ba za ta lalata dangantakar ta da Rasha ba.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya ba za ta iya yin watsi da huldar da ke tsakaninta da Rasha ko Ukraine ba, ya kara da cewa Ankara za ta cigaba da kulla yarjejeniyar kan iyaka domin hana barkewar rikicin.

Turkiyya mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO tana iyaka da Ukraine da Rasha a gabar tekun Black Sea kuma tana da kyakyawar alaka da juna. Ukraine ta bukaci a rufe tashoshin jiragen ruwa na Turkiyya.

Turkiyya ta mayar da martani mai kakkausar murya kan tsoma bakin na Rasha, inda ta bayyana matakin na soji da cewa “rashin adalci ne kuma ba bisa ka’ida ba” ta kara da cewa rikicin na da babbar barazana ga tsaron yankin mu da ma duniya baki daya.

“Muna Allah wadai da matakin soja na Rasha,” in ji shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani jawabi da yayi ta gidan talabijin a makon jiya.

4. Iran: Matsayin na Iran yana da bangarori biyu: wasu jami’an gwamnati sun ce sun yi Allah wadai da yakin, ko da yake wasu sassan Tehran na kallon kasashen yamma a matsayin masu tayar da rikici.

Fadada ayyukan kungiyar tsaro ta Nato babbar barazana ce ga tsaron kasashe masu cin gashin kai a yankuna daban-daban, in ji shugaba Ebrahim Raisi a wani taron manema labarai a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian ya rubuta a shafin shi na Twitter cewa rikicin Ukraine ya samo asali ne sakamakon batun fadada ikon kungiyar tsaro ta NATO, amma kuma ya rubuta cewa “ba mu yi imani cewa yaki zai magance wannan rikici ba”.

5. Brazil: Shugaba Bolsonaro ya ziyarci Moscow yan makonni kafin Rasha ta mamaye Ukraine, kuma har yanzu bai ce uffan ba

Shugabannin kasashen Latin Amurka sun soki Rasha kan kutsawar da ta yi a Ukraine, amma shiru da Brazil ta yi kan batun abin mamaki ne.

Shugaba Jair Bolsonaro, wanda kwanan nan ya gana da takwaran shi na Rasha a Moscow, bai ce komai ba game da daukar wani mataki kan yan kasar da suka makale a Ukraine.

Ma’aikatar harkokin wajen Brazil ta yi kira da a tsagaita bude wuta tare da warware matsalar diflomasiyya. Bugu da kari, ta bayyana kutsen a matsayin “cinye kan iyakokin Ukraine da karfin soji”.

Kazalika al’ummar yankin Latin Amurka sun yi watsi da sanarwar hadin gwiwa da kawancen da Amurka ke jagoranta suka yi na yin Allah wadai da kutsen da Rasha ta yi a Ukraine, wanda ke samun goyon bayan dukkanin kasashen yankin.

Bayan haka Brazil ta kada kuri’ar kin amincewa da tsoma bakin Rasha a Ukraine a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu.

6. Amurka: “Putin ya zabi ya yi wannan yakin, kuma shi da kasarsa za su biya farashi,” in ji Biden.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Rasha ta mamaye yankunan da ta mamaye ba tare da wata turjiya ko hujja ba.

Baya ga kakabawa Rasha sabbin takunkumi, Biden ya kuma ce zai tura dakaru zuwa Turai.

Sai dai shugaban ya ce sojojin Amurka ba za su shiga hannu kai tsaye da Rasha a rikicin na Ukraine ba.

7. Ingila: Boris Johnson ya zargi Rasha da kai hare-haren fararen hula a Ukraine. A wata ziyara da ya kai Poland a ranar 1 ga Fabrairu, Firayim Minista Boris Johnson ya ce Vladimir Putin yana daukar matakai “ga wadanda ba su da ilimi” a rikicin Ukraine.

Birtaniya ta dauki matakin ladabtarwa kan Rasha kuma tana tunanin korar ta daga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

8. Tarayyar Turai: Shugabar Hukumar Tarayyar Turai tana rike da tutar Uraine a cikin rigarsa yayin jawabinta a ranar 1 ga Maris

Baya ga yin tir da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, Tarayyar Turai ta yi kira ga mambobinta da su dauki matakin ladabtarwa kan attajiran Rasha da makusantan shugaban kasar. Ta kuma bukaci da su daina sayen iskar gas da mai daga kasar Rasha.

Sai dai shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy a ranar 1 ga watan Maris ya bukaci kungiyar tarayyar Turai da ta tabbatar mana da cewa kuna tare da mu, kwana guda bayan da ya bukaci kungiyar ta shigar da kasar shi cikin kungiyar.

Advertisement