Ɗan Wasan Senegal, Krepin Diatta Ya Caccaki Masu Yi Masa Dariya

Dan wasan Senegal, Krepin Diatta, ya caccaki jama’a musamman ‘yan Afirka da suka yi masa ba’a a lokacin gasar cin kofin Afrika da ta gabata. Ga abin da ya fada a shafukan sada zumunta:

“Na ji bakin ciki da na ga wasu ‘yan’uwa ‘yan Afirka suna min ba’a, ina yiwa nahiyarmu mai kyau da kauna, amma ba abin da nake samu sai cin fuska kawai, ba’a daga ’yan uwana, wannan abin naku yayi muni, kuma wariyar launin fata ta fito daga can.

Ina bukatan kwarin gwiwar ku ba zagin ku ba. Na gode wa duk wanda ya ba ni goyon baya. Allah ne kadai yasan karfina kuma ina alfahari da mutumtaka ta zahiri. Ba’ar ku ba za ta canza komai ba a rayuwata ba. Amma wani abu daya tabbata, shine dukkanmu ’yan Afirka ne.