Taskar LabaraiTsaro

Manyan Labaran Yau: An Dawo Intanet A Niger, An Gano Yan Gudun Hijara Na Bogi A Borno

Sadarwar intanet ta sake daidaita a jamhuriyar Nijar bayan katseta da hukumomin kasar suka yi tsawon kwanaki 10, sakamakon rikici da ya biyo bayan sakamakon zaben shugabancin kasar da ya bayyana dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum Muhammad a matsayin wanda ya lashe zaben.

Akalla mutane 2 suka rasa rayukansu yayin zanga-zangar da ta biyo bayan nasarar ta Bzoum Muhammad da ya lashe kashi 55.7 na kuri’un da aka kada, yayin da Mahaman Ousman na RDR Canji ya samu kashi 44.

An Gano Yan Gudun Hijara Na Bogi A Borno:

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa wani sansanin ƴan gudun hijira shigar ba-zata inda ya gano ɗaruruwan ƴan gudun hijirar na bogi.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta aike wa BBC ta ce daga cikin ƴan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji, 650 daga cikinsu na bogi ne.

Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS inda ake kula da mutanen ƙaramar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya raba da gidajensu.

EFCC Ta Gurfanar Da Surukin Tambuwal A Kotu Kan Zargin Sama Da Faɗi Na Miliyan 419:

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa waton EFCC ta gabatar da Sanata Umaru Tafida Argungu gaban Alƙali Mohammed Mohammed a babbar kotun jihar Sakkwato kan tuhuma ɗaya waton zarginsa da yin sama da faɗi da dukiyar jama’a da yawansu ya kai ₦419,744,612.30.

A cewar bayanin da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar ya ce tsohon Sanatan da ya waƙilci Kebbi ta Arewa a majalisa ta 6 ana zarginsa da yin kwana da hannun jari da gwamnatin Sakkwato ta saya da zai kai kashi 40 a Kamfanin Hijira wanda yake mallakar kamfanin Saƙa na Hijirah ne.

Paparoma Ya Ziyarci Jagoran Shi’a Na Iraqi:

Jagoran mabiya mazahabar Shi’a a Iraqi Ayatollah Ali al-Sistani ya yi kira ga hukumomi su kare ‘yancin Kiristoci a kasar bayan ganawarsa da babban limamin cocin Katolika Paparoma Francis a wannan Asabar.
A yayin ziyarar da Paparoma Francis din ya kai wa al-Sistani a garin Najaf da ke Iraqin, al-Sistani ya ce ya kamata Kiristoci su yi rayuwarsu kamar yadda kowane dan Iraqi yake da ‘yancin yin walwala a kasar.

Paparoma Francis din ya gode wa jagoran Shi’an na Iraqi, a kokarin da yake yi na ganin an kare rayukan tsiraru da ake gallaza wa a cikin al’umma.

Advertisement