Siyasa

Manyan jami’an Rasha da Ukraine zasu haɗu a Turkiyya don tattaunawa ranar Alhamis

Shugaban kasar Ukraine

Ministan harkokin wajen ƙasar Rasha Sergei Lavrov da takwaran shi na ƙasar Ukraine Dmytro Kuleba sun amince su haɗu a wani dandalin tattaunawa a kudancin Turkiyya ranar Alhamis, tattaunawar da zata kasance ta farko tsakanin manyan jami’an diflomasiyya tun bayan da kasar Rasha ta kaddamar da mamayar kasar Ukraine.

Mevlut Çavuşoğlu, ministan harkokin wajen Turkiyya ne ya bayyana hakan a yau Litinin inda yace zai halarci taron a birnin Antalya na shakatawa. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ita ma ra tabbatar da shirin.

Turkiyya memba ta NATO, wacce ke da iyaka da Rasha da Ukraine a cikin tekun Black Sea, ta yi tayin shiga tsakanin bangarorin. Ankara dai na da kyakykyawar alaka da Moscow da Kyiv, kuma ta kira mamayar da Rasha ta yi ba abin amincewa ba duk da cewa tana adawa da takunkumin da aka kakabawa Moscow.

Advertisement

Cavusoglu ya ce a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Lahadin da ta gabata, shugaba Tayyip Erdogan ya sake nanata tayin Turkiyya na karbar bakuncin taron kuma daga baya Lavrov ya amince.

Advertisement