Wasanni

Manchester United ta dakatar da Greenwood bayan zargin cin zarafi

Manchester United ta dakatar da dan wasan kwallon kafa Mason Greenwood, matakin da ya biyo bayan zargin da aka yi masa ta yanar gizo cewa dan wasan mai shekaru 20 ya ci zarafin wata mata.

A wata sanarwa ta farko da ta fitar ranar Lahadi, kungiyar ta ce tana sane da hotuna da kuma zarge-zargen da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda ta ce ba za ta kara yin tsokaci ba har sai an tabbatar da gaskiyar lamarin, ya kuma kara da cewa: “Manchester United ba ta amince da tashin hankali kowane iri ba.”

A wata sanarwa da ta fitar, United ta ce: “Mason Greenwood ba zai koma atisaye ba ko buga wasanni har sai an samu sanarwa.”

Advertisement

Zarge-zargen da ake yi wa Greenwood, da suka hada da bidiyo, hotuna da sakon murya, an sanya su a shafin Instagram a safiyar Lahadi kuma daga baya aka goge su.

Rundunar ‘yan sandan Greater Manchester ta ce an kama wani mutum da ake zargi da aikata laifin fyade da cin zarafi kuma ana tsare da shi a gidan yari domin amsa tambayoyi bayan da wata mata ta wallafa hotuna da bidiyo a shafukan sada zumunta da ke ba da labarin cin zarafi.

Kamar yadda ‘yan sanda suka yi ba su bayyana sunan wanda ake zargin ba.

“An sanar da manyan ‘yan sandan Manchester a safiyar yau game da hotuna da bidiyo na yanar gizo da wata mata ta buga da ke ba da rahoton abubuwan da suka faru na tashin hankali,” inji wata sanarwa.

“An kaddamar da bincike kuma bayan bincike za mu iya tabbatar da cewa an kama wani mutum mai shekaru 20 da ake zargi da aikata fyade da kuma cin zarafi,” inji sanarwar.

Greenwood ya zura kwallaye shida da taimakawa biyu a wasanni 24 da ya buga a duk gasar da United ta buga a bana.

Ya fara aikinsa a makarantar koyar da United kuma ya buga wa tawagar kasar Ingila wasa sau daya.

Advertisement