Siyasa

Mali ta kori jakadan Faransa saboda wasu kalaman adawa

Mali ta bai wa jakadan Faransa wa’adin sa’o’i 72 a ranar Litinin da ya fice daga kasar bayan kalaman “kalaman adawa da gwamnatin sojin kasar” da tsohuwar mulkin mallaka ta Faransa ta yi game da gwamnatin rikon kwarya, in ji sanarwar da aka karanta a gidan talabijin na kasar, kamar yadda gidan talabijin din Al-Jazeera ya habarto.

Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya fada a ranar Juma’a cewa gwamnatin mulkin sojan Mali “ba ta da iko” a daidai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin kasar Afirka ta Yamma da kawayenta na Turai bayan juyin mulki biyu.

Har ila yau Le Drian ya kira gwamnatin sojan da bata da hakki. Ministar tsaron Faransa Florence Parly ta fada a ranar Asabar cewa sojojin Faransa ba za su tsaya a Mali ba idan farashin ya yi yawa.

Advertisement

“Gwamnatin Mali ta yi kakkausar suka da kuma yin watsi da wadannan kalamai, wadanda suka saba wa ci gaban dangantakar abokantaka a tsakanin kasashe,” in ji wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

“Gwamnatin Mali ta sanar da jama’ar kasa da na duniya cewa a yau… an sanar da jakadan Faransa a Bamako, mai girma Joel Meyer… game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na neman sa ya bar kasar cikin sa’o’i 72.”

Babu wani sharhi kai tsaye daga Paris.

Advertisement