Uncategorized

Malamin Jami’a Yayi Ram Da Matar Shi Tare Da Wani Ɗalibin Shi A Otel

Wani malamin jami’a dan kasar Kenya ya fusata kuma ya ji takaici sa’ad da ya kama matar shi tana lalata da wani dalibi a wani otal da ke yankin.

An tattaro cewa mutumin ya jima yana jin labarin rashin imanin matar amma babu yadda za a yi ya tabbatar da hakan, sai dai a wata rana mai kaddara ya samu labarin cewa tana tare da masoyin ta a wani dakin otel.

Mata ta shiga otal din da ke Mosoriot, Nandi kuma an kama ta dumu-dumu da wani daliba da aka fi sani da Brian.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa mutumin yace matar shi ba ta kwana a gida a daren da ya gabata yayin da yaron ba ya zuwa karatu da rana.

An ce matashin dalibin yana karatu ne a kwalejin horar da likitocin kasar Kenya inda malamin ke aiki.

Bayan kama su, malamin ya kuma kunyata matar shi ta hanyar daukar hotuna da bidiyo.

Wani hoto da ya bayyana a yanar gizo ya nuna Brian baya sanye da rigar shi kawai domin bai da lokacin saka tufafin shi lokacin da malamin ya kutsa cikin dakin.

Yayin da matar mutumin ta rufe fuskar ta da kunya a lokacin da ya cigaba da kokarin nuna mata fuskar ta a kyamara kuma ya zarge ta da rashin aminci.

Madogara: https://www.correctng.com/lecturer-nabs-his-wife-in-hotel-room-with-his-student/

Free Bonus

X