Labarai
Malam Na Ta’ala Bai Rasu Ba, “Inan A Raye” – Inji Shi
Sanannen KannyWood, Malam Na Ta’ala wanda ke fitowa a shirin Dadinkowa ya musanta rahotannin dake yawo a shafukan sada zumunta na rasuwar shi.
Kafin yaɗa rahoton mutuwar Malam Na Ta’ala, jarumin yana kwance ne a wata asibiti inda yake jinyar rashin lafiya.
Bayan yaduwar rahotan mutuwar Na Ta’ala a kafofin sada zumunta kamar WhatsApp, Facebook da sauransu ne dai jarumin ya fito a cikin wani faifan murya da bidiyo inda ya ƙaryata wannan labari.