Al'umma

Makinde ya amince da nadin Balogun a matsayin Olubadan na 42 na Ibadanland

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da nadin Sanata Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 na Ibadanland.

Makinde ya amince da nadin ranar Litinin.

Idan zaku iya tunawa, kujerar sarautar Olubadan na Ibadan ta zama babu kowa akai a ranar Lahadi 2 ga watan Janairun wannan shekara.

Advertisement

Mukamin ya zama babu kowa ne saboda rasuwar Oba Saliu Akanmu Adetunji. Majiyoyi sun habarto cewa Makinde ya amince da nadin sabon sarkin.

Amincewar ta biyo bayan shawarar da Olubadan-in-Council ya bayar wanda kuma aka sanar da gwamnan kwanan nan.

Makinde, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Taiwo Adisa, ya yi fatan Allah ya ba Balogun lafiya da kwanciyar hankali.

“Na yi farin cikin sanar da nadin Otun Olubadan na Ibadanland, Babban Cif Lekan Balogun a matsayin Olubadan na 42 na Ibadanland.

Advertisement