Taskar Labarai

Majalisar wakilai ta karbi kudirin sauya sunan Najeriya zuwa UAR

Adeleye Jokotoye, mai ba da shawara kan haraji ne ya gabatar da shawarar ga kwamitin a taron sauraron kararrakin jama’a na Kudu maso Yamma da ke Legas a ranar Laraba, 2 ga Yuni, 2021.

Yayin da yake gabatar da wannan shawara, ya ce sunan Najeriya a yanzu sunan danniya da wadanda suka yi mulkin mallaka a baya suka yiwa kasar wanda kuma ya kamata a canza sunan yanzu.

Ya ce sauya suna ga kasar zai kasance a zahiri da kuma a hankali zai nuna cewa an shiga wani sabon babi.

“A wannan lokaci a cikin tarihin mu, ya zama wajibi mu canza sunan Najeriya don nuna sabuwar tafiya wanda za’a shigar dashi da sabon kundin tsarin mulki,” inji shi.

Limamin Coci Yayi Kira Ga Gwamnatin Najeriya Da Ta Ayyana Dokar Ta Baci Kan Rashin Tsaro

Da yake bayyana dalilin da ya sa ya zabi Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jokotoye ya ce Najeriya ta kunshi daruruwan kabilun da ke bukatar hadin kai.

Ya kara da cewa Nijeriya za ta iya zaɓar United Alkebulan Republic (ma’ana: United Mother of Mankind Republic) a matsayin sabon suna.

Mai ba da shawara kan harajin ya kuma ba da shawarar a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima don yin la’akari da tsarin hada-hadar kudi, tsarin jihohi ko na yanki da kula da biyan haraji, cire dokar rigakafi, da sake nazarin Lissafin Dokokin na Musamman.

Back to top button