Siyasa

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna daga mukamin shi

Ƴan majalisar dokokin jihar sun tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mahdi Aliyu-Gusau daga mukamin shi.

Advertisement

Arewa Times Hausa ta ruwaito cewa wani kwamitin da babban alkalin jihar, Mai shari’a Kulu Aliyu ya kafa, na binciken Aliyu-Gusau, bisa zargin shi da aikata muguwar dabi’a da cin zarafin ofis.

Mambobin kwamitin binciken sun hada da: Justice Halidu Tanko-Soba a matsayin shugaba, Oladipo Okpeseyi (SAN), Abdul-Atadoga Ibrahim (SAN), Hussaini Zakariyau, (SAN), Amina Tanimu-Marafa, Alhaji Sani Mande da Ahmad Buhari-Rabah.

Advertisement

Mataimakin gwamnan ya bayyana ‘yan majalisar a matsayin “jahilai” saboda rashin tilasta wa kotu umarnin cewa dukkan bangarorin su ci gaba da zama a kan lamarin.

Shugaban kwamitin ya mika rahotonsa ga kakakin majalisar, Honorabul Nasiru Muazu Magarya a ranar Laraba, inda ya ce kwafi biyu ne kawai aka fitar kuma kwamitin ba ta da ikon yin magana a kai.

Bayan da shugaban majalisar ya karanta wa majalisar rahoton, jim kadan bayan mika shi, mambobi 20 cikin 24 ne suka kada kuri’ar tsige mataimakin gwamnan.

Advertisement