Kasuwanci

Mai ya haura $100, yayin da Putin ya umarci jami’an nukiliya da su zama cikin shiri

Farashin danyen man fetur yayi tashin gwauron zabi a ranar Litinin kan karin takunkuman da aka kakabawa kasar Rasha kan mamayar da ta yiwa Ukraine, wanda hakan yasa shugaba Vladimir Putin ya sanyawa kasar shi takunkumin karya tattalin arziki.

Danyen mai yayi tsalle sama da dala $100 a ganga ɗaya, da farko ya kara sama da dala 7 a wata ɗaya, yayin da harkokin nukiliya da matsalolin biyan kuɗi na banki ke ƙara fargabar cewa jigilar mai daga sassan duniya na iya tabarbarewa.

Kasar Rasha ce ke da kusan kashi 10 cikin 100 na yawan mai a duniya.

Advertisement

Putin ya tayar da tarzoma a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ba da umarnin “dakaru masu karewa” na kasar Rasha – wadanda ke da makaman nukiliya – su shiga a cikin shirin ko-ta-kwana, yana mai nuni da kalamai masu zafi da shugabannin kungiyar tsaro ta NATO suka yi da kuma yawan takunkumin tattalin arziki da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha.

Rasha ta kira ayyukanta a Ukraine “aiki na musamman.”

Stephen Brennock na dillalan mai na PVM yace “Shawarar da shugaba Putin ya yi na sanya sojojin nukiliyar Rasha cikin shirin ko-ta-kwana lamari ne da ke nuna tashin hankali da damuwa wanda zai iya zama tallafi ga farashin mai.”

Advertisement