Kasuwanci

Ma’aikacin Majalisar Dokoki ta kasa da ya fado daga matakalar bene, ya mutu

Wani ma’aikacin Majalisar, Abdul Olajide Abayomi, ya fado daga bene a harabar majalisar kuma ya mutu ranar Litinin.

Abayomi, mai shekaru 34, ya yi aiki da Sashen Inter-Parliamentary a karkashin Hukumar Kula da Ka’idojin Tsare-Tsare na Majalisar Dokoki ta Kasa.

Shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa marigayin na kan hanyarsa ta zuwa hawa na biyu na bangaren fadar White House ne a lokacin da ya zame ya yi birgima.

Advertisement

Abokan aikin sa ne suka kai shi Asibitin Majalisar Dokoki ta kasa domin kula da lafiyarsa amma ya rasu a hanya.

Likitoci sun tabbatar da cewa ya mutu ne sakamakon kamuwa da bugun zuciya da kuma wasu cututtuka da yake fama da su.

Advertisement