Kasuwanci

Lokacin Daina Amfani Da Tsofaffin Kudi Yana Daram-Dam, Jan. 31

Jama’a da dama sun koka kan ranar da aka ba su ta daina amfani da tsofaffin kudin saboda ba a samun sabon kudin bayan ajiya.

Advertisement

Babban bankin na CBN ya bayar da ranar 31 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a bar amfani da tsofaffin kudin, kuma an raba sabbin kudaden ga dukkan bankunan, kuma har yanzu mutane ba su samu sabon kudin da aka sake fasalin ba.

Babban bankin na CBN ya ci gaba da cewa, an raba sabbin kudaden da aka yi wa kwaskwarima ga bankuna daban-daban a Najeriya, kuma duk bankin da bai fitar da sabon kudin da aka sake fasalin ba, to a sanar da shi domin sun tura wakilai da za su rika sanya ido a kan bankunan.

Advertisement

Wato bankin zai baiwa kwastomomin su da duk wanda ya nemi kudi sabon kudin da aka sake fasalin, haka kuma ana shawartar daidaikun mutane da su ajiye tsohon kudaden su domin kada su yi asarar kudaden su a karshe.

Duk wanda ya ajiye tsohon kudin zai karbi sabon kudin da aka sake fasalin a lokacin cirewa, har yanzu mutane na korafin cewa idan suka yi amfani da sabon kudin wajen sayen komai ba za a karbe shi a mafi yawan yankunan karkara ba.

Advertisement