Siyasa

Libya: Khalifa Haftar ya shiga takarar neman shugabancin kasar

Shugaban yakin kasar Libya Khalifa Haftar ya shiga takarar shugabancin kasar bayan ya bayyana a hukumance cewa zai tsaya takara a zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai zuwa, a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin, a ranar Talata.

Halifa Haftar wanda har yanzu yake rike da takardar shaidar zama dan kasar Amurka, yana fuskantar wata kotu a Virginia bisa zarginsa da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Tripoli, Benghazi, Derna, da sauran wurare a Libya.

Mai shigar da kara na sojin Libya ya kuma bukaci hukumar zaben kasar da ta dakatar da rajistar zaben Haftar da Saif Al-Gaddafi har sai an yi musu tambayoyi kan zargin aikata laifukan da aka shigar a kansu.

A cikin jawabin nasa na zaben shugaban kasa, Haftar ya ce ba shi da niyyar neman mulki ko wani mukami, amma shawarar da ya yanke na tsayawa takarar shugaban kasa na zuwa ne bisa bin ka’idojin dimokuradiyya da aiwatar da taswirar hanya da aka amince da ita. kuma bayan tawakkali ga Allah”.

Jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, dan Khalifa Haftar, Saddam, ya yi wata tafiya ta sirri a birnin Tel Aviv a ranar 8 ga watan Nuwamba, inda ya yi alkawarin kulla alaka da Isra’ila idan mahaifinsa ya jagoranci sabuwar gwamnatin da za ta karbi ragamar mulkin kasar bayan zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba.

Saddam Haftar ya kasance yana samun taimako daga kamfanonin hulda da jama’a (PR) da masu ba da shawara masu tushe a Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar wannan majiyar, ya kara da cewa wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa wakilan Haftar na aiki a wani kamfani da ke UAE tare da Isra’ilawa.

Sanarwar takarar na zuwa ne kwanaki biyu bayan Saif al-Islam Gaddafi, wanda ya yi rajista a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben kasar.

Matakin nasa na tsayawa takara zai fusata wasu da dama da ke zarginsa da neman kafa mulkin kama-karya na soji ta hanyar zabe bayan gazawar da ya yi na karbar mulkin kasar a 2019.

Back to top button