Al'umma

Laberiya: An kashe mutane da dama a wani taron addini kusa da Monrovia

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a wani taron addini da aka gudanar a unguwar da ke wajen babban birnin kasar Laberiya, a cewar jami’ai.

Advertisement

Kafofin yada labaran cikin gida sun bayar da rahoton a ranar Alhamis cewa, bala’in ya faru cikin dare a wurin taron da aka gudanar a filin wasan kwallon kafa a garin New Kru da ke arewacin Monrovia. Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da ya haddasa turmutsutsun ba.

Kakakin ‘yan sanda Moses Carter ya ce akalla mutane 29 ne suka mutu a bala’in amma adadin na wucin gadi ne kuma “zai iya karuwa”.

Advertisement

Mataimakin ministan yada labaran kasar ya ba da adadin wadanda suka mutu.

“Likitocin sun ce mutane 29 ne suka mutu, wasu kuma suna cikin jerin sunayen,” in ji Jalawah Tonpo, yayin da yake kira ga gidan rediyon jihar daga wani asibiti da ke kusa. Tonpo ya kara da cewa “Wannan rana ce ta bakin ciki ga kasar.”

Kafofin yada labaran cikin gida sun ce yara na cikin wadanda aka kashe a taron addu’o’in Kirista, wanda aka fi sani da ‘yan Salibiyya a Laberiya.

Ana sa ran shugaba George Weah zai ziyarci wurin a ranar Alhamis da yamma, in ji ofishin yada labaransa.

Shahararren mai wa’azi Fasto Abraham Kromah ne ya shirya taron na kwanaki biyu, wanda kuma ya ja hankalin jama’a da dama, kamar yadda hotuna da ke yawo a kafafen sada zumunta suka nuna.

Wasu ‘yan fashi da ke rike da wukake da adduna sun far wa masu ibada, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito, lamarin da ke nuni da cewa watakila hakan ne ya janyo turmutsitsin.

Wani shaidar gani da ido Emmanuel Gray, mai shekaru 26, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa ya ji “kara mai nauyi” a karshen taron, kuma ya ga gawarwaki da dama.

Hatsari da bala’o’i sun zama ruwan dare a Laberiya.

Advertisement