Tsaro

LABARI: An Sace Ɗaliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya Ta Lafia

An yi garkuwa da wasu dalibai hudu na Jami’ar Tarayya da ke Lafia a Jihar Nasarawa a kusa da harabar makarantarsu.

Arewa Times Hausa ta samu labarin cewa an yi garkuwa da daliban ne a unguwar Maraba.

Jami’in hulda da jama’a na cibiyar Abubakar Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin.

Advertisement

A cewarsa, ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar jami’ar ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis, inda suka garzaya da daliban zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Da yake mayar da martani, Mataimakin Shugaban Jami’ar (VC) Farfesa Shehu Abdul Rahman, ya yi kira da a gaggauta sakin daliban da aka yi garkuwa da su.

“Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman, a madadin masu gudanar da cibiyar, ya nuna matukar bacin ransa game da wannan lamari mai ban tausayi tare da yin Allah wadai da shi da kakkausar murya da neman a gaggauta sakin wadanda aka yi garkuwa da su.” sanarwar da Jami’ar ta karanta a wani bangare.

Advertisement