Siyasa

Kwankwaso Ya Bayar Da Sharadin Janyewa Daga Takarar Shugaban Kasa

Dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso ya bayar da sharadin da za ta iya sanya shi ficewa daga takarar shugaban kasa a 2023.

A cewar tsohon gwamnan jihar Kano, idan jam’iyyar ta samu nagartaccen dan takara, a shirye yake ya janye daga takarar.

Kwankwaso ya ce ba ya sha’awar zama shugaban Najeriya na gaba amma duk da haka ya yi amanna cewa shi ne ya fi cancantar tsayawa takarar.

Advertisement

Dan takarar jam’iyyar NNPP ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana sahihancin shi na siyasa a gidan Chatham a ranar Laraba.

Gidan Chatham shine Cibiyar Sarauta ta Burtaniya ta Harkokin Duniya.

Kwankwaso ya yi alkawarin inganta tattalin arzikin kasar tare da samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don bunkasa da kuma jawo jarin kasashen waje idan an zabe shi.

Ya ce, “Na gina ajujuwa sama da 500 a lokacin da nake gwamnan jihar Kano, kuma idan aka zabe ni zan kawo karin mutane a cikin jirgin domin magance bukatun ilimi a Najeriya.”

Dangane da rashin tsaro, Kwankwaso ya tuno lokacin da ya yi a matsayin shi na ministan tsaro kuma mai ba shugaban kasar Somalia shawara na musamman, ya kuma yi alkawarin kara daukar karin aiki a cikin sojojin Najeriya.

Advertisement