Siyasa

Kwanakin Da Suka Rage Kafin Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023

Yayin da ya rage kwanaki 80 kacal a gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2023, ana cigaba da tafka muhawara da nazari kan ‘yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa.

Idan dai ba a manta ba ana kallon Peter Obi da Asiwaju Tinubu da Atiku Abubakar da kuma Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin manyan ƴan takarar da zas su fafatawa a zaben.

Daga yau zuwa ranar zaɓen 2023 na shugaban kasa akwai sauran kwanaki 80 da suka rage kafin wannan ranar.

Advertisement
Advertisement