Kasuwanci

Kwanaki 90 Sun Isa Kowa Ya Kai Tsofaffin Kudin Shi Banki, Ba Zamu Kara Wa’adi Ba – CBN

Da yake jawabi ga jama’a yayin ganawa da manema labarai, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce kwanaki 90 sun isa a ajiye tsohon kudin zuwa bankuna.

Idan za a iya tunawa dai babban bankin ya ce tsohon jerin takardun kudi na Naira 200, 500 da 1000 ba za su sake yin amfani ba bayan ranar 31 ga watan Janairu, 2023, kuma mutane su ajiye su a bankuna kafin lokacin.

“Dole ne in faɗi haka abin takaici, ba ni da wani labari mai daɗi ga waɗanda suke ganin ya kamata mu canja wa’adin, a yi hakuri. Dalili kuwa shi ne kwanaki 90 ya isa waɗanda ke da tsohon kuɗin su ajiye a bankuna”. Yace.

Advertisement

Kalaman Godwin Emefiele dai ya jawo cece-ku-ce daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

-Adio Akeem ya ce bankuna na ci gaba da raba tsofaffin takardun kudi.

-Adebayo Kemi ya yarda da shi cewa kwana 90 ya isa. Ta kuma nufa kan masu sayen kuri’u, tana mai cewa ba za su yi nasara ba a wannan karon.

-Shi ma Solomon Rotimi ya amince da Emefiele.

Advertisement