Tsaro

Kwamandan Boko Haram Maras Imani, Rugu-Rugu, Ya Mika Wuya Ga Sojoji, Ya Bada Dalilai

Wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Malam Adamu Rugurugu, wanda aka bayyana a matsayin mai kisa, ya mika kan shi ga rundunar sojojin Najeriya a jihar Borno, inda yace ya yanke shawarar fitowa daga daji tare da mayakan shi da dama domin mika wuya sakamakon shiga tsakani da Gwamna Babagana Zulum yayi.

Rugurugu wanda a halin yanzu yana daya daga cikin sansanonin da gwamnatin jihar ta kafa domin karbar tubabbun ‘yan ta’adda, yace bayan da gwamnan ya shiga tsakani, sai ya gane cewa ya ja hanya ba daidai ba, sai ya yanke shawarar ya koma wani sabon ganye.

“Eh, ina daya daga cikin kwamandojin Boko Haram. Na samu sunan Rugurugu wanda ke nufin babu rahama daga fagen fama,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai da suka ziyarci sansanin a ranar Lahadi.

Advertisement

“A fagen fama, ina da haɗari sosai domin na kan lalata komai a hanya ta. Ban jin tsoro. Wadannan tabo da alamomin da kuke gani a kai jiki na duk sun faru ne saboda rashin tsoro.

“Gwamnan ya ji labari na kuma ya san cewa idan aka lallashe ni na fito, mayaka da yawa za su biyo ni, a haka muka fito muka mika wuya.

“A wannan sansani, zan ce gwamnati da Janar Abdel Ishaq suna yi mana abubuwa da yawa da suka mika wuya ga mayakan da suka mika wuya. Sun tabbatar min da cewa idan na yi watsi da wannan harkar da ba ta da wata fa’ida, za a biya mu.

“Ana kula da matan mu da yaran mu da kyau. Idan kowa ya kamu da rashin lafiya, muna da likitocin da za su yi musu magani,” inji shi.

Rugurugu na daya daga cikin ‘yan ta’adda sama da 14,000 da suka mika wuya da iyalan su da ake tsare da su a sansanoni daban-daban a Maiduguri da sauran sassan jihar.

Advertisement