Siyasa

‘Ku nuna cewa kuna tare da mu’ – Shugaban ƙasr Ukraine ya roƙi EU

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya shaidawa kungiyar Tarayyar Turai a ranar Talata, kwana guda bayan da Kyiv ta nemi shiga kungiyar a hukumance, yayin da take fafatawa da dakarun Rasha.

Ƴan majalisar Tarayyar Turai da dama sanye da rigar #standwithUkraine dauke da tutar Ukraine, wasu kuma dauke da gyale masu launin shudi da rawaya ko ribbon, sun yabawa Zelenskiy yayin da yake jawabi a zauren majalisar Turai ta hanyar bidiyo.

“Muna fafutuka ne domin mu zama membobi daidaikun Turai,” inji Zelenskiy a cikin yaren Yukren a cikin jawabin da wani mai fassara ya fassara wanda ya yi magana cikin hawaye.

Advertisement

“Ku tabbatar da cewa kuna tare da mu, ku tabbatar da cewa ba za ku bar mu ba, ku tabbatar da cewa ku Turawa ne, sannan rayuwa za ta yi nasara da mutuwa, haske kuma ya yi nasara a kan duhu,” in ji shi. ” EU za ta fi karfi tare da mu.”

Zelenskiy ya cigaba da zama a Kyiv don yin gangamin jama’ar shi don adawa da mamayar. A yayin da yake magana da yan majalisar dokokin Tarayyar Turai da manyan jami’ai, wani rukunin masu sulke na Rasha yana yin ta’adi a babban birnin Ukraine.

“Muna (tare da ku),” inji mataimakin shugaban hukumar Tarayyar Turai Maros Sefcovic yayin da yake mayar da martani ga rokon Zelenskiy, yana mai cewa EU za ta bai wa Ukraine makamai, bisa dorawa Rasha takunkumin da ba a taba gani ba, bayan da ta mamaye Ukraine a makon jiya.

Advertisement