Tsaro

Ku magance matsalolin da aka ambata, ku daina zagina – Ortom ya mayarwa fadar shugaban kasa martani

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya bayyana a ranar Laraba cewa, ya kamata fadar shugaban kasa ta dauki shawarwarin da ya bayar domin amfanin kasa baki daya, kuma ta daina zaginsa.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu a ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV ya caccaki Ortom kan yadda yayi watsi da kalubalen da jihar sa ke fuskanta da kuma yin suka ga shugaban kasa.

Ortom, yace ya kamata fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro da sauran kalubalen kasa da ya ke magana a kai, sannan ta daina zagin shi a matsayin dauke hankali.

Advertisement

Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Ortom, Nathaniel Ikyur, ya fitar tace: “Gwamnan ya koka kan yadda ake tauye hakkin yancin Najeriya a kullum da ayyukan Fulani makiyaya da ke cigaba da kashewa da korar al’umma a fadin kasar. Jihar Katsina ta shugaban kasa ta samu mummunar illa da ayyukan wadannan yan ta’adda. Kasawar da Shugaban kasa ya yi wajen tabbatar da tsaron Najeriya ne yasa yan ta’adda suka mamaye yawancin jihohin. Wannan kuma ba abin daGwamna Ortom janyo ba ne.

“Sama da shekara guda kenan an rufe Gwamna daga ganin Shugaban kasa. Wannan ma karya ce?

Advertisement