Kasuwanci

Ku Daina Karbar Tsofaffin Kudi – CBN Ya Shawarci Yan Najeriya

Babban Bankin Najeriya CBN ya umurci jama’ar kasar da su daina karbar tsoffin kudaden da bankunan kasuwanci ke ba su, saboda ganin lokacin daina amfani da su na kara karatowa.

Mataimakiyar Daraktan Sarrafa kudaden Bankin, Dr. Rakiyat Yusuf ta bayyana haka lokacin da take fadakar da ‘yan kasuwa a birnin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, dangane da sabunta takardun kudin da bankin ya yi a kwanakin baya.

Rakiyat ta ce, bankin na su ya tanadi hukunci mai tsauri akan bankunan kasuwancin da aka samu suna ci gaba da bai wa jama’a tsoffin takardun kudaden wadanda za su daina aiki daga ranar 31 ga watan Janairu.

Advertisement

Daraktar ta bukaci jama’a da su gabatar da korafi akan duk wani bankin kasuwancin da ya ci gaba da bai wa mutane tsoffin takardun kudaden ta kafar na’urar ATM, yayin da ta bukace su da gaggauta kai tsoffin kudaden bankin domin sauya musu da sababbi.

Jami’ar ta ce babu dalilin da bankunan za su ci gaba da bai wa jama’a tsoffin takardun kudaden domin babban bankin ya yi tanadi na musamman wajen wadata su da sabbin kudaden da aka buga.

Rakiyat ta yi bayani akan dalilan da suka sanya bankin sabunta kudaden da suka hada da dakile ayyukan ta’addanci da ayyukan masu garkuwa da mutane da cin hanci a tsakanin al’umma da kuma magance hauhawan farashin kayan masarufi.

Advertisement