Siyasa

Ku cigaba da amincewa da APC – Lawan ya roki yan Najeriya

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci yan Najeriya da su cigaba da mika amanar al’amuran kasar nan ga jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa APC ita ce jam’iyyar da za su amince da ita.

Lawan yayi wannan roko ne a ranar Lahadin da ta gabata a Legas a karo na biyar na shirin tallafawa mutane da Sanata Solomon Olamilekan Adeola wanda ke wakiltar Legas ta Yamma Sanata ke yi.

Taron wanda ya gudana a harabar kwalejin yan sandan Najeriya da ke Ikeja, taron ya samu halartan gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Advertisement

A wata sanarwa da mai bada shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi ya fitar, Lawan ya bayyana Legas a matsayin gida na jam’iyyar APC tare da bayyana kwarin gwiwar cewa “APC da yardar Allah za ta cigaba da mulkin Legas da mulkin Najeriya. ”

Abin da ya kamata mu yi shi ne mu ci gaba da abin da muke yi a yanzu. Ku tallafa wa shugabanninmu. Yi hakuri da mu. Haɗa kanmu kuma ba shakka, mu mai da hankali.

“PDP na iya gaya muku wani abu mai ban dariya game da gwamnatin APC a matakin kasa amma PDP ta mulki Najeriya tsawon shekaru 16 kuma duk abin da suka yi shi ne su bar mana gadon kalubale a 2015.