Laifuku

Kotun Ta Yanke Wa Ministan Buhari Hukunci Ɗauri A Gidan Yari

An yankewa tsohon ministan ma’adinai da karafa Uche Ogah hukuncin zaman gidan yari bisa samunsa da laifin yin takardun jabu.

Hukuncin Ogah na kunshe ne a cikin umarnin da wata kotun majistare ta jihar Abia da ke zama a Umuahia ta bayar a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba.

Kotun a lokacin da take yanke hukuncin ta bayar da umarnin a kamo Ogah tare da kai shi gidan yari a duk wata cibiya ta gyaran jiki mafi kusa a jihar Abia.

Advertisement

Jam’iyyar All Progressives Congress ta shigar da kara a kan Ogah bisa zargin cewa tsohon ministan duk da bai shiga zaben fidda gwani na gwamna da jam’iyyar ta gudanar a ranar 26 ga watan Mayu, ya fitar da sakamakon bugi.

APC a cikin karar ta mai lamba: No. UMSC/362/2022 ta kuma ce Ogah duk da cewa bai shiga zaben fidda gwani ba, ya cigaba da yin jabun sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar kai tsaye.

A cewar jam’iyyar Ogah ya yi hakan ne da nufin a yi aiki da shi a matsayin na gaskiya.

A cikin karar, mai shigar da karar ya bayyana cewa matakin da Ogah ya dauka na cin fuska ne ga jam’iyyar da kuma sahihin dan takarar gwamna a jihar Abia, Chief Ikechi Emenike.

Wanda ya shigar da karar yace Ogah ya aikata laifin da ya sabawa sashe na 465 na kundin laifuffuka (kamar yadda ya dace a Abia) da kuma hukunci a karkashin sashe na 467.

A hukuncin da ta yanke, Ngozi N. Nwangwa, majistare da ta jagoranci lamarin, ta ce wanda ake kara “yana da laifi kamar yadda ake tuhuma”.

Advertisement