Kotun Soji Ta Yankewa Mambobi 26 Na Kungiya Mai Dauke Da Makami Hukuncin Kisa A Congo
Wata kotun soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 26 da ake zargi da hannu a kungiyoyin masu dauke da makamai ciki har da kungiyar M23 bayan zaman wata babbar kotu da aka fara yi a karshen watan jiya.
An samu Corneille Nangaa, shugaban kungiyar Alliance Fleuve Congo (AFC) da laifukan yaki, da hannu wajen tayar da kayar baya da kuma cin amanar kasa.
Nangaa da wasu mutum 20 da ake tuhuma an yanke musu hukuncin kisa ne ba sa nan a ranar Alhamis, saboda a halin yanzu suna gudun hijira.
Shugaban kotun ya ce wadanda ake tuhuma biyar da suka halarci zaman kotun suna da kwanaki biyar don daukaka kara kan hukuncin.
Mai gabatar da kara a shari’ar da aka fara tun ranar 24 ga watan Yuli ya bukaci da a yankewa mutum 25 daga cikin wadanda ake tuhuma hukuncin kisa da kuma daurin shekaru 20 a gidan yari ga wanda ake kara.
Nangaa, tsohon shugaban hukumar zabe ta DRC, ya kaddamar da yunkurin siyasa da soja na AFC a watan Disamba da nufin hada kan kungiyoyi masu dauke da makamai, jam’iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula don adawa da gwamnati.
Daya daga cikin mambobinta ita ce kungiyar masu dauke da makamai ta M23 da ake zargi da kisan jama’a a rikicin gabashin DRC na tsawon shekaru da dama.
Muhimman mutane na M23 da ake yi wa shari’a sun hada da shugabanta Bertrand Bisimwa, da hafsan soji Sultani Makenga da kakakinta Willy Ngoma da Lawrence Kanyuka.
A cikin wani sako da ya aike daga wani wuri da ba a bayyana ba, Nangaa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, “wannan ra’ayi na shari’a yana karfafa gwagwarmayarmu don tabbatar da dimokiradiyya a Kongo”.
A watan Maris, gwamnatin Kongo ta yi fatali da suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama, tare da dage hukuncin kisa da aka yi tun shekara ta 2003, da nufin kai hari kan jami’an soji da ake zargi da cin amanar kasa.