Al'umma

Kotu ta yanke wa Malamin addini kukuncin kisa bisa laifin kashe abokin shi

Wata babbar kotun jihar Legas da ke da zaman ta a Tafawa Balewa ta yanke wa wani malamin addinin Musulunci mai suna Fatai Afobaje dan shekara 34 hukuncin kisa bisa samun sa da laifin kashe abokin shi tare da yanke gawar shi.

Mai shari’a Modupe Nicol-Clay a ranar Laraba, 17 ga watan Maris, ta yanke wa malamin hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin hada baki da kisan kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Arewa Times Hausa ta tattaro cewa alkalin kotun ya bayyana cewa, masu gabatar da kara, gwamnatin jihar Legas, ta tabbatar da karar ta da babu shakka.

Advertisement

Nicol-Clay yace masu gabatar da kara sun iya tabbatar da cewa wanda ake tuhuma yayi sanadin mutuwar abokin shi Rafiu Sulaiman mai shekaru 44.

An cigaba da tsare wanda ake tuhuma tun shekarar 2017
Tun a shekarar 2017 ne aka tasa keyar mai laifin, inda yaƙi amsa laifin shi.

Tawagar masu gabatar da kara, karkashin jagorancin Ms Adesola Adekunle-Bello, ta gabatar da shaidu shida tare da gabatar da shaidu 12 yayin shari’ar.

Masu gabatar da kara sun shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya kashe Sulaiman ne tare da yanke masa kai, hanji, huhunsa, dawa da hannaye.

Lamarin ya faru ne a watan Fabrairun 2015, a kauyen Itire Village Magbon, Badagry, jihar Legas.

Laifukan sun ci karo da sashe na 221 da 231 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2011.

Advertisement