Siyasa

Kotu Ta Umurci Hukumar Zaɓe, INEC Da Su Dawo A Cigaba Da Rijistar Masu Zaɓe

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta cigaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR) har zuwa kwanaki 90 kafin zaben 2023.

Arewa Times ta ruwaito a watan Agustan 2022 cewa hukumar ta dakatar da cigaba da rijistar masu kada kuri’a (CVR).

An ga wannan a shafin yanar gizon hukumar.

Sai dai a hukuncin da ya yanke a ranar Talata, Mai shari’a Inyang Ekwo ya kuma umarci INEC da ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya da suka cancanta ba su rasa damar samun katin zabe a zabe mai zuwa ba.

A cewar Mista Ekwo, alkalan zaben na da aikin da kundin tsarin mulki ya ba su na tabbatar da cewa tsarin ya bi dukkan dokokin da suka dace a Najeriya.

Advertisement