Wasanni

Kotu Ta Tura Tsohon Dan Wasan Naya Na Barcelona Gidan Yari

Kama Dani Alves kan zargin fyade ya haifar da girgizar zukata a matakai da dama, tun daga wasan kwallon kafa zuwa siyasa.

Haka nan ya haifar da ɗimbin martani yayin da dangin shi suka shafa.

Ku tuna cewa an kama Alves a ranar Juma’a a Barcelona bayan an zarge shi da cin zarafin wata mata a wani gidan rawa na dare.

Advertisement

Dan wasan mai shekaru 39 ya musanta aikata laifin a lokacin da yake magana da kafar yada labarai ta Spain Antena 3 a farkon wannan watan Janairu.

Dan kasar Brazil, wanda kuma ya taba bugawa Juventus wasa da Paris Saint-Germain, ya bayar da sanarwa ga rundunar ‘yan sandan Mossos d’Esquadra ranar Juma’a kafin ofishin mai shigar da kara ya bukaci a tsare shi kada a ba shi beli.

Advertisement